Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa manyan kasar nan ba su taba goyon bayan tafiyar siyasar sa da kuma muradin sa na neman zama shugaban kasa ba.
Ya ce don haka su gode wa talakawan Najeriya da suka rika fadi-tashin goyon bayan sa, har ya zama shugaba, wanda a yanzu ga shi ya ceto kasar nan daga durkushewa.
Buhari ya ce a duk lokacin da takara ta bijiro, sai manyan kasar nan su tsaida dan takarar da suke gani zai kare muradin siyasar su da kuma dukiyoyin sa.
Ya ce amma su talakawan kasar nan, sun fahimci irin son kai na manyan kasar shi ya sa suka jajirce a kan sa, ba tare da dora masa wasu sharuddan da zai cika musu idan ya zama shugaba ba.
Haka Buhari ya bayyana a cikin hirar da aka yi da shi a Gidan Talbijin na NTA: “Na yi takara sau uku kafin na yi nasara a karo na hudu. Manyan kasar nan su gode wa talakawa wadanda su ne suka zabe ni.”
Buhari ya kara da cewa irin gagarimin goyon bayan da ya samu daga talakawa, wani babban tukuicin ne a gare shi, wanda manyan ‘yan siyasa masu tarin kudi ba su iya samu daga talakawan.
“Babu wata karamar hukumar da ban taba zuwa ba kasar nan tun daga 2003, lokacin da na fara kamfen zuwa yanzu.”
Discussion about this post