Zanga-zanga ta tilasta Omar Al-Bashir na Sudan sauka daga mulki

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Omar Al-Bashir na Sudan ya sauka daga muki, bayan an shafe kwanaki ana matsa masa lamba da zanga-zanga, babu kakkautawa.

Jaridar Alarabiya ta UAE, ta ce Al-Bashir ya mika mulki ga Majalisar Kolin Sojojin Kasar, jiya Laraba da dare.

Al-Bashir ya shafe shekaru 30 ya na mulkin kasar Sudan, tun bayan da ya kwace mulki cikin 1989, a lokacin ya na soja.

Sudan ce kasa mafi fadi a Nahiyar Afrika, kuma ita ce bakin ruwan Kogin Nilu, wanda ya raba wasu kasashen Afrika da Saudi Arabiya.

Sai dai kuma wasu jaridu sun ruwaito cewa Al-Bashir ya mika mulki ne a daren jiya, bayan da sojoji suka kewaye fadar sa.

Hakan na nuni da cewa akwai yuwuwar ko dai sojojin ne suka tirsasa shi yin murabus, ko kuma juyin mulkin ruwan sanyi suka yi masa.

Alkadari da farin jinin Al-Bashir ya zube a kasashen Turai da Amurka, tun bayan da Kotun Kasa Da Kasa ta zarge shi da laifin yi wa al’ummar Yankin Dafur kisan-kiyashi.

Kasashen Afrika sun goya masa baya, tare da cewa sharri da bi-ta-da-kulli Turawan Yamma da Amurka ke yi masa.

Dalili ma kenan suka ki bada goyon bayan damka shi a hukunta a kotun da ke birnin Hague.

Shi ne shugaban Sudan da ya fi dadewa a mulki, tun bayan samun ‘yancin kasar cikin 1956.

Share.

game da Author