Tsarin “TARAYYA” na kara hargitsa Arewa, Daga Hassan Ringim

0

A karnin da Christopher Columbus ya ziyarci tsibirin Carribean na San Salvador wanda har a karshe aka samu kasar da a yanzu ake kira Amurka, a daidai lokacin al’ummar wata nahiya a Afrika, wato al’ummar arewacin Najeriya sun san me suke yi ta fannin zamantakewa da sauran al’amura a gargajiyance, daga baya su Mai Aloma da Muhammadu Rumfa suka bayar da kofar kafuwar addinin islama da har yanzu ake yin sa a matsayin hanyar tsira duniya da lahira.

Abubuwan da dama sun faru a tarihi, masu dadi da akasin haka, har zuwa jallin mamayar da turawa suka yi mana, suka kakaba mana dokoki da bin duk abin da suke so, kuma suka fara jirkita da sauya mana dabi’unmu da kuma sauran al’adu da addini ma baki daya. A haka har aka kai mu da sunan mun samu ‘yancin kai, aka rada mana suna Najeriya.

Kafin samun ‘yancin kai, bayan an hade yankin kudu da arewa a 1901, zuwa 1914 aka kaddamar da hakan a hukumance, abubuwa da dama sun faru. Da yake ba tarihi zan bayar a rubutun ba, ina ganin ya kamata ya tabo batun Mr. Bernard.

A shekarar 1939, Mr. Bernard Bourdillon ya raba Najeriya zuwa yanki uku da sunan Lardina uku na tarayyar Najeriya. Hakan bai samu tagomashi ba, sai a shekarar 1946 a cikin kundin tsarin mulkin Mr. Richard. A takaice daga 1901 zuwa 1958, shekaru biyu kafin samun ‘yancin kai, larduna 2 zuwa 3 kawai aka samar, kuma kowanne na da ‘yancin sa daidai gwargwado.

Daga wancan lokaci na 1958 zuwa yanzu 2019, lardina ukun nan, an daddatsasu har sun haifar da jihohi sama da 30 da kuma kananan hukumomi sama da 700. Shin a wannan sauyi ko ci gaba da aka samu ya zamarwa Arewa gata ne ko kuwa? Abin da nake son haskakawa kenan!

Kamar yanda kalmar mulkin TARAYYA ko hadaka yake nufi, gwamnati ta sama ko ta tsakiya a gwarance, na bayar da damar kowanne bangare ko yanki da ya zartar da abubuwan da suka kamaci yankinsa wanda kuma ba zai sabawa manufar tarayyar daga wani bangare ba. To wannan sarkakiya da aka shiga ita ce ta jefa yankin Arewa a cikin wani yanayi mara dadi sama da shekaru 50 da samun ‘yanci daga Ingila.

Abu guda da zan yi magana akan sa shine Ilimi. Shin Ilimin ko damar yin ilimi da karatu a Arewa ya dace da yanayin da aka sameta tun asali ko kuwa? Alal misali, a baya an taso da karatun allo, da asuba za a fara karatu har hantsi, a ci gaba da yamma zuwa magariba idan aka dauke Alhamis da Juma’a. To bayan zuwan Boko an dubi wani tsari da za a bawa wancan karatun allo kariya da gata, yanda ba zai samu matsala ba? Ba ayi hakan ba, akan hakane, aka fara cewa Boko, Bokoko a wuta. Hatta Bokon ma ana nufin na bogi ko na karya. Matsala ta farko kenan.

Duk wani ci gaba da za ayi a duniya ta fuskar STME ne, wato Science, Technology and Mathematical Education. Kuma dole sai ta hanyar boko za a cimma hakan.

Illar da tarayya ta samarwa Arewa a bangaren Arewa shine, an nuna Curriculum ko Manhajar karatu zai zama bai daya ne baki daya a duk kasa. Sai dai wasu darussa da za su bambanta. Misali koyar da Arabic ko Hausa, a Kudu kuma Igbo ko CRK haka. Amma a hakikanin nazarin, shin bukatun Arewa da Kudu daidai ne ta fuskar samar da ilimi? A’a, to kun ga kenan yi mana kudin goro a bangaren bukata daga tarayya zai zamar mana kalubale.

Yanzu ace daga fara boko a Arewa, an hada da tsarin Tsangaya ga masu ra’ayin ba za su bari yaransu su yi boko ba. Ace a cikin makaranta ga ajujuwan masu tsangaya ga na boko zalla. Kuma malaman addinansu a basu kulawa da karin matsayi daidai da bukatar yanayi da kuma aikinsu, to da yanzu ba wani almajiri da za a gani yana gararamba a titi da sunan karatun allo ko almajirci.

Abu na gaba, da mun gyara wannan tsari, to batun wasu su shigo mana da hayaniyar Boko Haram bai taso ba. Domin kuwa yara sun taso sun ga an watsar da malamansu, kudin shigarsu shine kawai idan sun yi addu’ar suna ko mutuwa ko kuma rubutun-sha. Amma rana daya wani yayi boko ya gama sakandare yayi diploma an bashi aiki, ya fara more duniya, dole alamar tambaya ta shiga zukatan mutanen. A karshe idan malaman suka ga za su rasa makomar abincin su, sai su ce ai boko haram ce, dole mu yake su, barayi ne, dagutai da sauransu. Sauran kasashen da suke son nakasta kasa, sai su kawo tallafi, shikenan sai a rasa zaman lafiya a kasa.

Daga karshe, magana ta gaskiya, dole sai an mike an shiga majalissa an sake duba tasirin tarayya ga makomar Arewa. Tun daga kan karatun firmare zuwa jami’oi sai an ga wani tsari da gyara za ayi don su dace da addininmu. Domin maganar gaskiya, batun ace addini ba zai ci gaba da tasiri ga zamantamewarmu da karatun mu ba, tamkar muna yaudarar kan mu ne wallahi.

Ayi duba na tsanaki, me zai iya yiwuwa da kuma akasin haka. Sai a samu mutane masu ilimi da boko ba gyauron turawa ba, su sake duba fasalin kasa da yankuna, kowa a bashi dama daidai da tunaninsa da kuma addininsa, yanda matsaloli irin su tayar da kayar baya, tsauraran akidun addini da aikata munanan laifuka za su ragu a sannu a hankali.

Share.

game da Author