Yadda dandazon kudan zuma ya kashe wani jami’in Kwastan

0

Hukumar Kwastan ta bada sanarwar mutuwar wani babban jami’in ta, wanda ya rasa ran sa sanadiyyar harbin kudan zuma.

Abubakar Abba ya rasa ran sa a lokacin da wani dandazon kudan zuma ya baibaye shi, sannan ya yi ta sakar masa harbi, a lokacin da ya ke sintiri a dajin Ashipa, kan iyakar Seme da ke yankin Badagry, a Legas.

Kakakin Jami’an Kwastan na Seme, mai suna Saidu Abdullahi, ya fitar da sanarwar cewa al’amarin ya faru ne a ranar Talatar da ta wuce, lokacin da Abba ke bakin aikin sa na sintiri.

Hukumar Kwastan ta kuma nuna takaicin rashin Abba, wanda ta nuna cewa hazikin jami’in kwastan ne, wanda bai taba fashin zuwa aiki ba.

Ta yi addu’ar Allah ya sa aljanna ce makomar sa, tare kuma da yi wa iyalan sa da iyayen sa ta’aziyya.

Hukumar ta Kwastan ta bayyana cewa Abba dan asalin Jihar Yobe ne. An yi wa gawar sa jana’za, kuma aka rufe shi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Share.

game da Author