KUDIN MAKAMAI: Kotu za ta fara zaman hukunta Sambo Dasuki da su Bafarawa

0

Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Hussein Baba-Yusuf, ya sa ranar 11 Ga Yuni ta zama ranar da zai fara zaman shari’ar tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki da Bashir Yuguda a zargin facaka da naira bilyan 19.4 na kudin makamai da suka yi.

EFCC ta maka Dasuki, Yuguda tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa kotu.

An kuma maka har da dan Bafarawa mai suna Sagir, da kuma wani kamfani maisuna Dalhatu Investment Limited.

Ana zargin su da laifuka 25 wadanda suka danganci cin amana, facaka da kudi kimanin naira biliyan 19.4.

An dage karar ne zuwa 11 Ga Mayu, saboda lauyan Bafarawa mai suna Lateef Fagbemi ya shaida wa kotu cewa babban lauyan Dasuki bai samu halartar zaman kotun ba, saboda mutuwar matar dan sa.

Bayan Mai Shari’a ya tabbatar da rasuwar matar, sai ya sa bangaren lauyoyin biyu suka zauna, su ma suka tabbatar da rasuwar ta.

Daga nan ne ya aza ranar 11 Ga Mayu, domin a ci gaba da shari’a.

Tun bayan kama Dasuki a cikin 2015, har yau ba a sake shi ba, ya na tsare.

Share.

game da Author