FARMAKI: Boko Haram sun kashe sojoji biyar, sun jikkata wasu, da dama kuma sun bace

0

A wani harin samame da Boko Haram suka kai kan wani sansanin sojojin Najeriya a Jihar Barno, sun kashe soja biyar tare da ji wa wasu sojoji masu yawa rauni.

Ana fargabar akalla an kashe soja biyar tare da wasu da dama da aka ce an ji wa rauni a lokacin da maharan Boko Haram suka kai samame a sansanin jojin.

An kai wannan farmaki ne a ranar 26 Ga Afrilu, a wani sansanin sojojin Najeriya da ke Mararrabar Kimba, kimanin kilomita 130 nisan wurin da Maiduguri.

Sojojin Bataliya ta 254 ne wadanda ke a karkashin Birgade na Sojojin Musamman na 25 ke kula da wurin.
Dukkan su kuma zarata ne da ke karkashin ‘Operation Lafiya Dole.’

An ruwaito sojoji takwas sun jikkata sosai, sannan kuma an kwashi manyan makamai an tsere da su. Kamar dai yadda wata majiyar cikin sojoji ta bayyana wa PREMIUM TIMES.

‘RASHIN NAGARTATTUN MAKAMAI DA MOTOCIN KAI HARE-HARE’

Da farkon barkewar gumurzun dai sojojin Najeriya sun ja daga an yi ta gwagwagwa da su da Boko Haram, amma can da wuta ta yi wuta, sai suka gudu zuwa cikin daji.

Wannan kuwa ya faru ne saboda makaman da sojojin ke amfani da su a lokacin ba su da ingancin garambawul sosai. Haka dai wata majiya ta bayyana.

Har yanzu ba a hakkace ko soja nawa ba ne ba a gani ba tukunna, ya zuwa yau Talata da safe. Amma majiyar da ke cikin sojoji ta ce wadanda har yanzu ba a gani ba sun fi dozen daya, idan za a yi kidayar dozin-dozin.

Ba a kuma tantance ba ko wasun su sun koma sansanin su, amma dai tuni aka tura zaratan nema da kuma ceto suka bazama aikin neman su.

Haka dai majiyar mu ta tabbatar.

Wadanda aka kashe da wadanda aka ji wa raunuka duk an kwashe su zuwa wata cibiyar kula da sojoji marasa lafiya a Maiduguri, tun a ranar 27 Ga Afrilu.

“Sojoji sun nuna jajircewa da kuma tsananin kishin fafatawa da Boko Haram, amma sai aka ci karfin su saboda kayan yakin su ba su da garambawul, kuma motocin su sun lalace ana cikin fama.”

Haka wani babban jami’in soja ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Sai dai kuma ya ki yarda ko amincewa a bayyana sunan sa, saboda har yanzu mahukuntan soja ba su sanar da kai harin ba tukunna.

SAMAMEN ’YAN-MUTUWA-DOLE

Maharan Boko Haram sun shammaci sojojin yayin da suka darkake su a cikin motocin harba manyan bindigogi samfurin tashi-gari-barde har mota 15. Sun kuma arce da wasu motoci na sojoji da gurneti da bindigogi da harsasai, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar.

Kakakin Hedikwatar Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya bai amsa kiran wayar da wakilin PREMIUM TIMES ya yi masa ba, domin jin ta bakin sa ba.

Amma wani jami’in hulda da jama’a na sojojin ya shaida cewa manyan kusoshin soja na “nazarin abin da ya biyo bayan harin da Boko Haram din suka kai.”

Boko Haram sun kai wannan harin ne a daidai yanayin da sojoji ke yawan nanatawa da murnar gagarimar nasarar da suka samu wajen karya lagon Boko Haram.

Share.

game da Author