Hukumomin Saudiyya sun saki Zainab Aliyu

0

A sanarwa da mai taimakawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai Bashir Ahmad ya fitar, hukumomin Saudi Arabiya dake tsare da Zainab Ahmad sun sake ta.

Bashir ya bayyana haka ne a shafin sa ta twitter inda ya kara da cewa nan ba da dadewa ba ma’aikatan harkokin kasahen waje za ta yi wa ‘yan Najeriya bayani akai.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya umarci Antoni Janar na Tarayya, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da ya gaggauta shiga cikin lamarin halin da Zainab Aliyu ke ciki a hannun mahukuntan kasar Saudiyya.

Zainab, wadda dalibar jami’a ce, wadda ke tsare a hannun mahukuntan kasar Saudiyya bayan an samu wata jaka mai dauke da kwayoyi kuma jakar na dauke da suna da lambar tikiti duk na sunan Zainab Aliyu din.

An samu jakar ne a filin jirgi bayan sun sauka kasar Saudiyya da niyyar Umrah.

Sai dai kuma Gwamnatin Najeriya, ta hannun Hukumar Hana Fataucin Kwaya sun shaida cewa bincike ya nuna Zainab ba ita ce ta fita da kwayar ba.

An gano wani gungun mutane masu sana’ar safarar kwayoyi zuwa Saudiyya, ta hanyar rubuta sunan wani matafiyi, a matsayin jakar kwayar tasa ce.

Tuni aka bada sanarwar kama wasu mutane shida masu hannu a safarar kwayar ta hanyar makala sunayen wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

Mai ba Shugaba Buhari Shawara a Harkokin ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri ce ta bayyana wa PREMIUM TIMES haka, ta hannun jami’in yada labarai na ta, Abdur-Rahman Balogun, a ranar Litinin.

Share.

game da Author