Kotu ta sallami Gwarzo, Shugaban Hukumar Hannayen Jarin Kamfanoni

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sallami Shugaban Hukumar Kula da Hannayen Jarin Kamfanoni (SEC), Munir Gwarzo.

Mai Shari’a ya kuma wanke shi tare da Babban Kwamishinan Hukumar, Zakwanu Garba, bayan kasa samun su da aikata laifukan zambar da aka yi zargin sun aikata.

Hukumar Ladabtar da Ma’aikata (ICPC) ce ta maka su Gwarzo kotu a gaban Mai Shari’a Husseini Baba-Yusuf, inda aka tuhume su da laifin harkallar kudade da kuma azurta kan su da makudan kudaden gwamnati.

Tsohuwar Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ce ta dakatar Da Gwarzo da kuma Garba, tun a cikin Nuwamba, 2017.

Daga nan Ministar ta kafa kwamitin bincike, bayan nan kuma ICPD ta maka su kotu.

Amma da ya ke yanke hukunci yau Talata a kotu, Baba Yusuf ya ce ICPC ta kasa gabatar da kwakkwarar shaida hujja ko da guda daya da kotu za ta ita gamsuwa cewa wadanda ake tuhuma din sun aika laifin da aka zarge su da aikatawa.

Ya kara da cewa shaidun da ICPC ta gabatar wa kotu, ba su nuna tabbatacin Gwarzo da Garba sun aikata wani laifi ba.

Ya ci gaba da cewa dukkan abin da aka yi zargin Gwarzo ya aikata, ya samu amincewa ne daga Hukumar Gudanarwar SEC, wadda halastaccen abu ne kenan ya aikata.

Shaidu hudu da aka gabatar duk sun kasa bayar da shaidar da kotu za ta iya kama Gwarzo da Garba da laifi.

Sannan kuma a waje daya, wasu masu baya hujja sun yi baki biyu, wato ba’asin da kowanen su su hudun ya bayar, ya sha bamban da na kowa, maimakon a samu bayanan shaidar da suka bayar ya yi daidai da na kowa.

Batun zargin ya kafci kudi ya sai mota kuwa, kotu ta gamsu da shaidar da wadanda ake kara suka gabatar cewa doka ta ba Gwarzo damar sayen motar da zai rika hawa a matsayin sa na Shugaban SEC.

Share.

game da Author