Kungiyar ‘Victims Support Fund (VSF)’ ya tallafa wa mata 17,000 wadanda suka yi fama da hare-haren Boko Haram a Arewa Maso Gabashin kasar nan da jarin Naira 20,000 domin inganta rayuwar su.
Shugaban kungiyar Sunday Ochoche ya fadi haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ochoche ya bayyana cewa VSF ta tsara shirin tallafa wa mata a fannin sana’o’i da farfado da aiyukkan gona domin inganta rayukan mutanen da hare-haren Boko Haram ya shafa a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan.
” Mun fara da tallafa wa mata masu sana’o’in hannu 100 da Naira 20,000. A yanzu dai wannan shiri ya tallafa wa mata 17,000 da jarin Naira 20,000 da aka zabo daga sansanoni 10 dake yankin.
Ochoche ya ce a fannin aiyukkan gona kuma VSF za ta tallafa wa mata da maza dake noman rani da damuna da kuma wadanda ke kiwo.
Ya ce a fannin gona VSF za ta samar da taki, iri, magungunan feshi da sauran su wadanda manoman za su bukata sannan a fannin kiwata dabbobi VSF za ta horas da masu kiwata dabbobi musamman masu kiwon awaki kan yadda za su iya siyar da nonon awakin su domin siyarwa.