Da misalin karfe tara na yammacin Lahadi ne wasu mahara da ake zargin Fulani ne suka kai wa kauyen Numan-Chuko dake karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa hari inda su ka kashe mutane 15 sannan wasu mutane takwas suka sami rauni a jikinsu.
Wata mazauniyar kauyen mai suna Maiwuya Bahago ta bayyana wa manema labarai cewa maharan sun far wa kauyen ne a daidai ana wani bukin taron suna.
Ya’ya na hudu ne suka rasu a wannan hari domin duk sun halarci wannan taron buki.
Maiwuya ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo musu dauki. Ta ce da yawa cikin wadanda suka sha a wannan hari tsofaffi ne sannan kuma talakawa ne.
Wani matashi da maharan suka harba a kafa mai suna Maikasuwa Ngila ya tabbatar wa manema labarai cewa Fulani ne suka kai wa mutanen kauyen hari a yammacin Lahadi.
” Daga shigowan su sai suka fara harbi ta ko ina.
Bayan haka jami’in asibitin Akwanga Gonji Thomas ya bayyana cewa asibitin ta karbi gawar mutane 15 sannan tana duba wasu mutane takwas da suka sami rauni a dalilin harin.
” Mun salami hudu daga cikin mutane takwas din da suka sami rauni saura hudun ne ke kwance a asibitin.
Sarkin Akwanga Chum-Mada Akwanga Samson Yare ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa jami’an tsaron jihar da manyan kayan aiki domin tunkarar wadannan mahara.
A karshe, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Inusa Mohammed yace rundunar ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan mummunar abu.