Hukumar Zabe ta maida wa Shehu Sani martani

0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta maida wa sanatan dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya martani bisa korafin da yayi wai daya daga cikin layoyin da hukumar ta nada yana da kyakkyawar alaka da gwamnan jihar Kaduna ne, Nasir El-Rufai.

Idan ba a manta ba, sanata Shehu Sani ya garzaya kotun sauraren kararrakin zabe don shigar da kara na rashin amincewa da sakamakon zaben sanata ta Kaduna ta tsakiya.

Shehu Sani ya ce an tafka magudi a zaben sannan anyi ta aringizon kuri’u a wasu kananan hukumin da ke karkashin wannan shiyya.

A korafin sanata Shehu Sani, yace lauyan da hukumar zabe ta nada domin ya kareta yana da kyakkyawar alaka da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da hakan zai sa ba za ati masa adalci ba.

Hukumar zabe ta ce ba ta zabi lauyoyin da za su mata aiki ba bisa alakar su da wani dan siyasa.

Hukumar ta ce zai iya yiwuwa akwai wadanda suka yi wa aiki a baya amma wannan ba dalili bane da zai sa ace suna so su nuna son kai a shari’ar.

Shehu Sani na jam’iyyar PRP ya sha kayi a zaben sanata da aka yi na shiyyar Kaduna ta Tsakiya a hannun Mal Uba Sani na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PRP ta zo na uku a sakamakon zaben da aka bayyana inda Lawal Adamu na Jam’iyyar PDP ya zo na biyu.

Share.

game da Author