Jirgin kasa ya markade wasu mutane biyu a Kano

0

A ranar Talata ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna ya sanar cewa jirgin kasa ya yi ajalin wasu mutane biyu a jihar.

Haruna ya ce wannan abin tashin hankali ya faru ne da misalin karfe takwas na safiyan ranar Talata a bayan watagidan shakatawa dake karamar hukumar Nasarawa.

” Mun zo mun ga cewa jirgin kasan ya raba jikin wadannan mutane biyu amma mun kwashi abinda muka iya samu na jikin su zuwa asibiti.

” Har yanzu dai muna gudanar da bincike domin sani jinsi da sunayen mutanen da jirgin ya markade.

Haruna ya yi kira ga mutane da su rika nesanta kan su daga kusantar layin jirgin sannan su rika gaggauta kaucewa daga hanyar idan suka ji kugin sa ya nan zuwa.

Share.

game da Author