Wata budurwa ta gamu da ajalinta ranar Lahadi bayan saurayin ta a dalilin bakin kishi ya bindigeta da bindigar sa kawai wai don ta amsa kiran wani namiji.
Budurwar ‘yar shekara 34 mai suna Victoria Ekalamene yar asalin jihar Bayelsa ne.
Victoria tana da shagon saida kayan masarufi a unguwar su, hasalima ita ce ke kula da saurayin mai suna Munabo Tonworio dan shekara 28.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Asinim Butswat ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari.
Bustwat ya shaida cewa tuni ‘yan sanda suka tasa keyar Munabo domin ci gaba da yin bincike akai.
Ya kara da cewa an samu bindigar da yayi amfani da wajen harbe wannan budurwa tasa sannan kuma an gano cewa ashe an dade ana farautar sa bisa hannu da ake zargin yana da shi a wasu ayyukan matsafa a jihar.
Discussion about this post