Buhari ya sa baki domin ceto ran Zainab Aliyu daga mahukuntan Saudiyya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Antoni Janar na Tarayya, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da ya gaggauta shiga cikin lamarin halin da Zainab Aliyu ke ciki a hannun mahukuntan kasar Saudiyya.

Zainab, wadda dalibar jami’a ce, wadda ke tsare a hannun mahukuntan kasar Saudiyya bayan an samu wata jaka mai dauke da kwayoyi kuma jakar na dauke da suna da lambar tikiti duk na sunan Zainab Aliyu din.

An samu jakar ne a filin jirgi bayan sun sauka kasar Saudiyya da niyyar Umrah.

Sai dai kuma Gwamnatin Najeriya, ta hannun Hukumar Hana Fataucin Kwaya sun shaida cewa bincike ya nuna Zainab ba ita ce ta fita da kwayar ba.

An gano wani gungun mutane masu sana’ar safarar kwayoyi zuwa Saudiyya, ta hanyar rubuta sunan wani matafiyi, a matsayin jakar kwayar tasa ce.

Tuni aka bada sanarwar kama wasu mutane shida masu hannu a safarar kwayar ta hanyar makala sunayen wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.

Mai ba Shugaba Buhari Shawara a Harkokin ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri ce ta bayyana wa PREMIUM TIMES haka, ta hannun jami’in yada labarai na ta, Abdur-Rahman Balogun, a yau Litinin.

Dabiri ta ce Buhari ya bada umarnin Ministan Shari’a Malami ya shiga cikin lamarin domin a ceto yarinyar, tun cikin makonni biyu da suka gabata, bayan an kai masa labarin abin da ya samu yarinyar.

Ta kara da cewa har zuwa yanzu dai ba a gurfanar da Zainab a kotu ba.

Sannan kuma a bisa hujjojin da ke gaban gwamnati na wadanda ke da hannu a cikin harkallar ba Zainab ba, akwai dalilai da hujjoji na ceto ran Zainab.

Mahaifin ta Habib Aliyu, ya yi roko ga Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Najeriya da Kungiyoyin Jinkai na Duniya da a gaggauta ceto ran ’yar sa daga mahukuntan Saudiyya.

Ya kuma nuna bacin ran cewa har yanzu yarinyar ta na kulle duk da kwakkwarar hujjar cewa ba ta da laifi.

Batun cewa an kama ta da kwayoyin Tramadol a Saudiyya, Habib yace zancen banza ne, domin da jaka daya tal Zainab ta shiga jirgi.

Zainab daliba ce a Jami’ar Maitama Sule University da ke Kano. Ta tafi Saudiyya ne tare da ’yar uwar ta.

Share.

game da Author