A yammacin Litini ne mahara dauke da makamai suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja, inda suka bude wa motar shugaban hukumar UBEC na kasa.
A wannan hari da suka kai, sun kashe direban sa sannan sun yi garkuwa da shi kan sa shugaban hukumar Mohammed Mahmood tare da ‘yar sa.
An aikata wannan abin tashin hankali ne a garin Katari, da misalin karfe 3:30 na yamma, kamar yadda wani hadimin Mahmood din ya sanar. Sannan ya kara da cewa har yanzu maharan ba su tuntube iyalan Mahmood din ba.
Discussion about this post