MACIJI: Najeriya ta samu wadatan maganin saran majici – Dafur

0

Jami’in hukumar raba maganin dafin maciji na Najeriya Nandul Durfa ya bayyana cewa hukumar ta wadatu da kwalaben maganin saran maciji akalla 4000.

Durfa ya ce samun maganin da hukumar ta yi ya kawo karshen matsalar karancin sa da hukumar da asibitoci ke fama da shi.

” A lokaci na yanayin zafi ne aka fi fama da matsalar saran macizai. Kuma har rayuka akan rasa a dalilin karancin magani da ake fama dashi a kasar nan. Sannan kuma wadanda ake samu ma sai an dauki tsawon lokaci kafin a shigo da su daga kasashen waje.

Ya ce Najeriya za ta iya magance wannan matsala ne idan ta fara sarrafa wannan magani a kasar nan a maimakon siyowa da take yi daga kasashen wajen.

“A yanzu haka kasashen duniyan da suka kware wajen sarrafa wannan magani a shirye suke domin su horas da mutanen kasar nan amma gwamnatin tarayya bata mai da hankali ba wajen ganin hakan ya yiwu.

Share.

game da Author