Shugaba Muhammadu Buhari ya sha wa ‘yan Najeriya alwashi cewa zai yi dukkan iyakar kokarin da zai yi domin rubanya ayyukan raya kasa a zangon san a biyu.
Buhari ya yi wannan alwashi jiya Litinin a Abuja, inda kuma ya kara nuna farin cikin sa da godiya ga ilahirin wadanda suka zake zaben sa.
Ya yi wannan jawabi a lokacin da Kwamitin Amintattun Gidauniyar Jihar Katsina suka kai masa ziyara domin taya shi sake lashe zabe.
Ya yi ikirarin cewa irin dandazon jama’ar da suka rika halartar gangamin kamfen din sa a duk jihar da ya je, ba jama’ar da wani zai ma yi tunanin cewa za a iya sayen su da kudi ba ne.
Galadiman Katsina, tsohon Babban Mai Shari’a Mamman Nasir ne ya jagoranci tawagar.
Buhari ya sake tunatar musu da cewa ya taba rike shugabancin Gidauniyar Jihar Katsina, a tsawon shekaru 17, inda a lokacin gidauniyar da gudanar da gagarimin aikin tallafa wa bangaren imi, kiwon lafiya da kuma aikin noma, musamman ga masu karamin karfi.
Da ya ke na sa jawabin, Galadiman Katsina ya ce Gidauniyar Jihar Katsina na kara godiya ga Allah da ya sake bai wa Buhari damar sake shugabancin kasar nan a shekaru hudu masu zuwa.
Ya kuma gode da irin muhimmiyar gudummawar sadaukar da lokaci da Buhari ya yi a shugabancin da ya yi wa Gidauniyar Jihar Katsina.