TASHIN HANKALI: Yadda mahara suka yi garkuwa da dandazon matafiya a titin Kaduna-Abuja ranar litini

0

Abu dai kamar ya zo karshe, sai gashi yana ya dawo kamar yau a ka fara.

A ranar Litinin ne masu garkuwa da mutane suka bude wa matafiya wuta a babbar titin Kaduna Zuwa Abuja.

Wannan hari da suka kai yayi matukar munin gaske domin bayan hadarurruka da aka yi tsakanin motoci, sun tafi da mutane masu yawan gaske cikin daji sannan sun yi wa mutanen da suka fada fashin gaske.

Wani matafiyi mai suna Yakubu Mohammed ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun tafi da matafi da dama cikin kungurmin daji.

” Zan tafi jihar Legas ne daga Kaduna. A daidai mun isa garin Katari sai muka iske wadannan mutane. Karfe shida da kusan rabi kenan na yamma. Abin dai babu dadi domin masu garkuwan sun fito da dayawan su daga cikin wannan daji bayan sun rika harbin motocin matafiya ta ko-ina.

” Daga baya sai ga motocin sojoji nan da na ‘yan sanda sun kariso wannan wuri. Kafin mutane suka iya wuce wa.

Yanzu dai kiri-kiri hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja ya zama bita da alwalanka domin maimakon ace ana samun sauki abin sai kara tabarbarewa ya ke yi.

Abin ya yi matukar baci da saukin da ake samu shine na jirgin kasa da yake balaguro a wannan hanya.

Matafiya sun koka kan sakacin gwamnati game da wannan abu da yake faruwa domin bai kamata ace hanyar da ta hada garuruwa da babban birnin tarayyar Najeriya ya zama tashin hankali ba.

Share.

game da Author