Ahmed Musa ya sake zama gwarzon dan wasa na 2019

0

Kaftin na ’yan wasan Super Eagles, Ahmed Musa ya sake zama Gwarzon Dan Wasan Najeriya a karo na biyu a jere.

Ya lashe wannan gasar ce da aka bayar da kyaututtukan ta jiya Litinin a Lagos, wadda kamfanin Aiteo/NFF ce ke shirya ta.

Gasar karo na farko ma da ake shirya a Lagos, Ahmed din ne ya lashe ta cikin 2018.

An ware sunayen fitattun ‘yan wasa uku, Ahmed Musa, Odion Ighalo da Alex Iwobi, inda Musa ya yi nasara a kan su.

Sannan kuma Ahmed din necdai ya lashe kyautar Kwallon da ta fi Burgewa, inda a nan ya doke Ighalo da Kevin Itoya.

Kwallon da Musa ya ci kasar Iceland ce ta janyo masa nasarar cin kyautar kwallon da ta fi burgewa.

Austin Okocha ne ya karbi kyaututtukan a madadin sa.

A bangaren mata kuwa, Onome Ebi ce ta zama gwarzuwa, inda ta doke Asisat Oshoal da Francsca Ordega.

Daga cikin tsoffin fitattun ‘yan wasan Najeriya da suka halarci bikin bayar da kyauttutukan akwai Taribo West, Ben Iroha, Finidi George, Mutiu Adepoju, Daniel Amokachi, Uche Okechukwu, Agustine Equavoen, Peter Rufai, Alloy Agu, Austin Jay-Jay Okocha, Sunday Oliseh, Samson Siasia, Nduka Ugbade da kuma Edema Fuludu.

An kuma karrama marigayi MKO Abiola a wurin taron.

Share.

game da Author