ZABEN KANO: ‘Yan daba sun Fatattaki mutane da ‘yan jarida a unguwar Gama

0

Wasu ‘yan jarida sun sha da kyar bayan wasu gaggan ‘yan daba dauke da makamai sun fatattake su a daidai suna kokarin yi wa masu zabe tambayoyi gama da zaben.

Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa ba a bar su sun shiga wurin kada kuri’ar ba. Ya ce suna isa wurin aka fatattake da muggan makamai sannan kuma wasu.

Wani dan jarida ya bayyana cewa a masallaci ya fake bayan an fatattake shi da sharbebiyar takobi.

” Wannan abu dai da kunya matuka domin ace wai zaben ma da ya kamata a yi cikin kwanciyan hankali wasu sai sun tada hankalin mutane.

Share.

game da Author