TARIN FUKA: Za a fara yin gwaji domin gano masu dauke da cutar a jihar Kwara

0

Hukumar hana yaduwar tarin fuka da kuturta reshen jihar Kwara ta bayyana cewa daga ranar Lahadi 24 ga watan Maris hukumar za ta fara yin gwaji domin gano mutanen dake dauke da cutar a kananan hukumomi uku dake jihar.

Wadannan kananan hukumomi su hana da Kaiama, Baruteen da Pategi dake mazabar Kwara ta Arewa.

Jami’in hukumar Mohammed Rasheed ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a inda ya kara da cewa hukumar ta amince ta wayar da kan mutane game da cutar yayin da take gudanar da binciken.

” A ranar tarin fuka da ake yi duk ranar 24 ga watan Maris hukumar mu ta amince ta gudanar da bincike domin gano mutanen dake dauke da cutar tare da wayar da kan mutane game da cutar. Burin mu shine samun nasara wajen dakile yaduwar cutar a jihar da kasa gaba daya.

” Alamun cewa an kamu da wannan cuta sun hada da rashin iya cin abinci, rama, tari, ciwon kirji, zazzabi da sauran su.”

Share.

game da Author