A yau Asabar ne ake maimaita zabuka a rumfunan zabe 208 daga cikin kananan hukumomi 29 wadanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce an yi aringizon kuri’u ko kuma an soke wasu kuri’un, har zaben ya zama wanda bai kammalu ba.
Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar PDP ne a kan gaban Gwamna Abdullahi Ganduje da ratar kuri’u sama da 26,655 bayan kammala kidaya.
A yau ana s ran masu jefa kuri’a 128,831 ne za su yi zaben da ake so bayan kammalawa a tantance wanda ya yi nasara.
Daga cikin wadanda za su yi zaben ne Ganduje zai nemi ya fara taras da Abba yawan kuri’un da ya yi masa rata, wato 26,655, sannan kuma ya nemi wuce shi, idan har zai iya.
Zai yi matukar wahala a tsere wa Abba da yawan kuri’u, domin a zaben da ya gudana makonni biyu da suka gabata, mutane sama da milyan biyu suka yi zabe. A cikin su ne Abba ya yi wa Ganduje ratar sama da dubu 26.
Shin zai iya yiwuwa Ganduje ya yi wa Abba ratar da zai yi nasara a kan sa a cikin adadin masu zaben da ba su kai 130,000 ba.
Kuma daga cikin wadanda za su yi zaben, bai yiwuwa a ce kowa ya fito jefa kuri’a saboda a tarihin zaben Najeriya, wadanda ba su fito ba, sun fi wadanda suka fita jefa kuri’a yawa.
Abba ya na tinkaho da abubuwa hudu, wato karfin siyasar Sanata Rabi’u Kwankwaso, Guguwar Kwankwasiyya, farin sa da kuma karfin karbuwar sa ga dandazon matasa.
Babban karfin da Gwamna Ganduje ke takama da shi, bai wuce karfin gwamnati ba. da wannan karfin mulki ya yi amfani a cikin mako daya kacal yayi wa Mazabar Gama ayyukan da ba a yi mata sama da shekaru 20 ba.
Daga cikin ‘yan takarar biyu, hankalin Ganduje ya fi tashi, ganin yadda ya ke ta fagamniya bakin-rai-bakin-famar ganin sai ya koma kan kujerar sa.
A jajibirin zabe, wato jiya Juma’a da dare, an yi zargin cewa jam’iyyar APC ta dauko sojojin hayar ‘yan tauri daga cikin kauyukan Kano da kuma makwabtan jihohi.
Alamomin haka sun fara tabbata ganin yadda aka rika samun rahotannin jami’an tsaro sun kama ‘yan daba a daren.
Sannan kuma dandazon ‘yan daba da aka tabbatar su na dauke da makamai, an yi ta watsa rahotannin cewa sun shiga cikin Mazabar Gama, wadda nan ce za a fi mamaita zabe a rumfuna masu yawa.
Dama kuma tun bayan da aka INEC ta ce za a sake zabe a wasu rumfuna, an kama wasu da aka yi zargin su na bi wasu mazabu su na sayen kuri’un jama’a.
Mazabar Gama nan ce mazabar Mataimakin Gwamna, Nasiru Gawuna, a cikin Karamar Hukumar Nasarawa.
Sai dai kuma a zaben gwamna da aka gudanar makonni biyu da suka gabata, Gawuna bai ci akwatin runfar zaben sa ba.
Jihar Kano na da Kananan Hukumomi 44, kuma a cikin 28 ne za a sake zaben a wasu rumfunan da aka kayyade mutane 128,831 kadai za su yi zabe.
Zaben ya na da tasiri sosai a siyasar Kano, ganin yadda masu ruwa da tsakin jihar suka gargadi wasu gaggan ‘yan siyasa da daga wasu jihohi cewa kada wanda ya sake ya yi musu katsalandan a siyasar su ta Kano.
Ba don haka ba kuwa, da yanzu an yi wa Kano irin taron dangin da aka yi wa jihar Osun a zaben ranar 22 Ga Satumba, 2018, wanda aka maimata zabe a wata mazaba daya.
Ko dai ya za ta kasance ce, jihar Kano ta kusa yin sabon ango. Ko dai tsohon mijinta Ganduje, ko kuma sabon ango Abba, Abba Gida-gida Abba.