Zababben gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, Kauran Bauchi ya bayyana cewa inganta rayuwar jama’an jihar Bauchi ne zai sa a gaba kafin wani bukatar sa a tsawon wannan mulki na sa .
Ya jinjina wa kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara bisa irin dimbin goyon bayan da ya nuna masa a wannan fafatawa da aka yi.
” Ina mai godiya a gareku mutanen jihar Bauchi bisa irin wannan halasci da kuka nuna min. Ina mai tabbatar muku cewa ba zan baku kunya ba. Zan rike kowa a matsayin daya sannan zan yi muku aiki domin dawo da martabar jihar Bauchi.
” Dole in jinjina wa kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, da wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin Allah ya bamu nasara a wannan tafiya.
Sanata Bala ya kara da cewa gwamnatin sa za ta maida hankali ne wajen bunkasa ayyukan noma da kasuwanci. Sannan da inganta Ilimi da samar da ayyukan yi a fadin jihar.
” Wani abu da faranta min rai shine ganin irin mataimakin da na dauka, wato sanata Baba Tela haziki ne kuma ya wakilci jama a majalisar dattawa. Hakan zai bamu daman tsara ayyukan ci gaba ga mutanen jihar Bauchi.
Da yake bayyana sakamakon zaben Malamin zabe na jihar Bauchi Mohammed Kyari ya ce Sanata Bala ya samu kuri’u 515,113, sannan gwamna mai ci Muhammed Abubakar ya samu kuri’u 500, 625.