Kungiyar ‘Nigerian Optometric Association’ (NOA) ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan samar da kiwon lafiyar ido mai nagarta ga mutanen kasa.
Shugaban kungiyar Ozy Okonokhua ne ya yi wannan kira ganin cewa ba kowa bane ke iya samun wannan kulan a asibitocin kasar nan.
Okonokhua yace abin takaici ne yadda mutane musamman mazauna karkara ke makancewa saboda rashin samun ingantaccen kulawa.
Ya ce gwamnati za ta iya shawo kan wannan matsalar ne idan ta samar da kula na ido a asibitoci domin mutane.Sannan ta wayar da kan mutane kan su rika garzaya wa asibiti domin duba idanuwar su.
A kwanakin baya ne Babban likita a asibitin koyarwa na jami’ar Ilori, jihar Kwara Dupe Ademola-Popoola ta yi tsokaci kan yadda iyaye zasu kare ‘ya’yan su daga kamuwa daga cutar makanta.
Ta ce a binciken da ta gudanar ta gano cewa iyayen yaran da suka kamu da cutar makanta sukan boye su a gidajensu har sai sun yi girman da za su iya fita bara.
Likita Popoola ta ce gwamnatin jihar ta kafa doka da zai tilasta wa iyayen kananan yara daga shekara biyar zuwa kasa da su kai su asibiti domin gwajin cutar makanta kafin su saka su a makaranta.
Domin mara wa wannan shiri na gwamnati baya, hukumar USAID ta tallafawa gwamnatin jihar da na’urorin gwajin ciwon ido.
Malama Popoola ta ce gwamati ta kaddamar da asibitoci 4 domin gwajin masu dauke da cutar makanta da kuma gwaji ga yara kanana.
Bayan haka kuma wadannan asibitoci za su zamo makaranta ga malaman asibiti domin koyar da yadda za’a kula da yara kanana musamman wadanda suke dauke da cutar makanta da kuma neman gwaji.