NAZARI: Jiga-Jigan ‘yan siyasa shida da zaben 2019 ya ladabtar

0

Iyayen gida a siyasance su ne hamshakan ‘yan siyasa wadanda suaka gina kan su cikin siyasa, sannan kuma suka gina wani gungu ko garken mabiya wadanda suka kewaye su domin ya rika amfani da su ya na cinma wani buri a cikin al’umma.

Sau da dama idan ana batu na siyasa, to sai dai mutum ya bi ra’ayin su. Su ke tsayawa takara a babban mukami, kuma su ne ke tsaida ‘yan takara a kananan mukami daga cikin yaran siyasar da ke kewaye da su suna yi musu fadanci.

A zaben da aka gudanar na 2019 a ranar 23 Ga Fabrairu da kuma 9 Ga Maris, wasu iyayen gidan siyasa sun kare kujerun su, wasu kuma igiyar ruwa ta tafi da su.

PREMIUM TIMES ta zakulo wasu gaggan iyayen gida a siyasa wadanda ambaliya ta ci a zaben 2019. Daga cikin su akwai:

BUKOLA SARAKI

Saraki ta kasance suna ne na wata daular siyasa a jihar Kwara. Kafin karfi ko bayyanar Bukola Saraki, mahaifin sa Olusola Saraki, wanda ya yi shugabancin majalisar dattawa a lokacin Jamhuriya ta Biyu a mulkin Shagari, ya yi karfin da sai da ta kai duk mai son yin nasara a jihar Kwara, to sai dai ya shiga jam’iyyar Saraki, mahaifin Saraki na yanzu.

Daga 1979 zuwa yau, Gidan Siyasar Saraki ya samar da gwamnoni shida a Jihar Kwara.

Sai dai kuma an kawo karshen wannan daular siyasa ta Saraki a aaben 2019, inda aka kayar da dan takarar gwamnan PDP na jihar Kwara, Saraki wanda ke shugabancin Majalisar Dattawa, kujerar da mahaifin sa ta taba hawa, shi ma ya fadi zaben sanata.

Saraki ya yi gwamnan jihae Kwara, daga 2003 ta hanyar goyon bayan mahaifin sa. Bayan ya kammala zangon sa biyu, cikin 2011 ya ki goyon bayan ‘yar uwar sa Gbemisola ta zama gwamna. Maimakon haka, sai ya goyi bayan gwamna da ke kai a yanzu, wato Abdulfatai Ahmed.

An kayar da Gbemisola ba da son ran mahaifin Saraki ba, wato Olusola Saraki.

Daga ranar a Saraki zai sauka idan an rantsar da Shugaban Kasa, Saraki zai zama dan kallo a siysar Najeriya, har zuwa shekara hudu idan an sake kada wata sabuwar gangar siyasar.

GODSWILL AKPABIO

Shi ne tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, jihar da ta fi kowace jiha arzikin man fetur, in banda Jihar Rivers. Ya yi gwamnan jihar tsawon shekaru takwas. Cikin 2015 bayan kare wa’adin sa kuma Sai ya ci takarar sanata.

Sai dai kuma komawar sa jam’iyyar APC ba ta amfana masa ba, domin an kayar da shi a zaben sanata, kuma APC ta fadi zaben gwamna a jihar Akwa Ibom.

Duk da irin karfin magoya bayan da ya gina a lokacin da ya na gwamna, ya kasa cin zaben sanata a wannan zabe na 2019.

GEORGE AKUME

Shi ma wani gogarman dan siyasa ne wanda zaben 2019 ya yi tafiyar ruwa da shi.

Tun da aka zabe shi gwamnan jihar Benuwai a karkashin PDP cikin 1999 ya kama ragama da linzamin siyasar Benuwai ya rike kam. Sai yanzu linzamin ya sabule daga hannun sa, dokin kuwa yay i masa kayen da ba zai iya tashi ba har sai bayan shekara hudu sai sake yunkurawa ya jaraba.

Lokacin da ya na gwamna, shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, kuma bayan ya kammala znagon san a biyu, ya shiga Majalisar Dokoki cikin 2007, ya sake cin zabe a 2011.

Ya shiga can ne a 2011, kuma a karkashin ta ya ci zaben sanata a shekarar.

Cikin 2015 kuma ya sake cin zaben sanata a karo na uku, duk dai mai wakiltar Jihar Benuwai ta Arewa.

Akume ne ya tsaya wa Gwamna Samuel Ortom ya ci zaben gwamna a 2015. Sai dai kuma bambancin ra’ayi dangane da rikicinnmakiyaya da manoma ya sa sun raba hanya.

Ortom ya koma jam’iyyar PDP, shi kuma Akume ya tsaya a APC bai fita ba, amma kuma yanzu a zaben 2019 bai yi nasara ba.

Bayan rashinn nasarar da ya yi, duk kuwa da cewa ya na cikin APC tsundun, APC din kuma ta rasa jihar Benue a zaben gwamna da na shugaban kasa.

IBIKUNLE AMOSUN

Duk da cewa Amosun ya samu nasarar zaben sanata da ya tsaya, ya kasa wajen taimaka wa jaron sa da ya tsaida takarar gwamna yin nasara.

Amosun ya zama sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya, amma kuma wanda ya tsaida a karkashin APM bai yi nasarar zama gwamna ba.

Gwamna Amosun ya samu matsala da uwar jam’iyyar APC a Abuja, bayan da ya tsaida dan lelen sa Adekunle Akinlade takarar gwaman, domin shi zangon sa biyu sun kare kenan.

Wannan bai yi wa Tinubu da wasu dadi ba. su kuma su ka tsaida Dapo Abiodun.

ROCHAS OKOROCHA

Kamar Gwamna Amosun, shi ma gwamna Okorocha dan takarar wata jam’iyyar ya goyi baya, kuma shi bai fice cikinn APC din ba.

Hakan kuwa ya faru ne saboda uwar jam’iyya ta goya wa dan takara Hope Uzodimma baya, shi kuma Okorocha ya kafe ya ce sai surikin sa zai tsaida takara, tunda ya kammala nasa wa’adin a matsayin gwamnan jihar Imo.

Dan lele kuma surikin Okorocha, Uche Nwosu ya fice daga APC ya koma jam’iyyar AA.

Sai dai Okorocha da Nwosu har ma da Hope Uzodimma na APC duk ba su yi nasara ba, domin jam’iyyar PDP ce ta yi nasara a jihar.

Da farko an bayyana cewa Okorocha ya yi nasarar lashe zaben sanata na Imo ta Yamma, amma kuma jami’in zabe mai bayyana sakamao, ya ce ‘yan takifen Okorocha ne suka tilasta shi bayyana cewa Okorocha ne ya yi nasara.

Don haka INEC ta soke hukuncin da ta bayar cewa Okorocha ne ya yi nasara.

ABIOLA AJIMOBI

Ya zama gwamnan jihar Oyo cikin 2011 a karkashin ACN. Sannan kuma ya sake cin zabe cikin 2015, a karkashin APC.

Ajimobi ya samu karbuwa a APC a fadin kasar nan. Har saka shi aka yi cikin masu sasanta rikicin jam’iyya.

Sai dai kuma can a gidan sa jihar Oyo, ya bari APC ta shiga cikin matsaloli, har ta kai da dama ‘yan jam’iyyar magoya bayan tsohon gwamna marigayi Lam Adeshina sun fice daga jam’iyyar, wasu kuma suka koma PDP.

Adawa ta yi zafi a jihar Oyo tun a wurin zaben fidda gwani. A zaben gwamna kuma an harbe dan majalisar tarayya har lahira.

Daga karshe dai APC ta rasa gwamna a jihar Oyo, inda PDP ce ta yi nasara, haka kuma Ajimobi bai yi nasara ba a takarar neman sanata da ya fito.

Share.

game da Author