Naziru ya yi sabuwar wakar Kira ga Buhari da ya saka baki a zaben kano a bai wa mutane zabin su

0

Fitaccen mawakin Sarkin Kano, Naziru Ahmed ya fitar da wata sabuwar waka da yake kira ga shugaba Buhari da ya saka baki a zaben Kano, ya toshe kunnuwar sa ya tabbata an baiwa mutanen jihar Zabin su.

Naziru a sabuwar wakar sa da ya fitar ranar Alhamis, ya roki Buhari da ya saka baki a zaben Kano.

Ya kara da cewa ana kokarin danne wa mutanen abinda suka zaba.

A wakar, Buhari ya roki Buhari da ya saka baki a wannan zabe ya tabbata an bai wa mutane zabin su.

Idan ba a manta ba jihar Kano na daga cikin jihohin da za a gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Maris.

Sauran jihohin da ba a kammala zaben gwamnan ba sun hada da Jihar, Filato, Bauchi, Adamawa, Sokoto da jihar Benuwai.

A jihar Kano abin yayi zafi da sai da aka rika kai ruwa rana tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun da ke fafatawa a zaben, wato APC da PDP.

A dalilin haka sai da ‘yan sanda suka tsare mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna da kwamishinan Kananan hukumomin jihar, Sule Garu. Daga baya an sake su.

A sakamakon da aka riga aka bayyana, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’u sama da Miliyan daya.

An bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta baiwa APC rata shine ya sa zaben bai kammalu ba.

Share.

game da Author