Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga zababbun ‘Yan Majalisar Dattawa da su hanzarta su fara aiki a kan sabon fasalin zarin zabe a kasar nan, da zaran sun shiga majalisa nan wata uku.
Yakubu ya furta haka ne a yau Alhamis a lokacin da ya ke damka wa kowane zababben sanata satifiket na shaidar lashe zabe.
“ Ina kira a gare ku da cewa da kun shiga majalisa, farkon abin da za ku yi shi ne zama domin yin aikin da ya kamata na kammala tsara fasalin zaben da a gudanar na 2023.”
Yakubu ya shaida musu cewa ba da dadewa ba INEC za ta fara hada nazarin da ta yi dangane da zaben 2019, ta yadda za a yi saurinn fahimtar alkiblar da zaben 20123 zai fuskanta domin fara shiri tun da wuri.
Idan ba a manta ba, majalisa ta aika wa Shugaba Muhammadu Buhari kudirin gyaran dokar zabe, amma ya ki amincewa ya sa mata hannu, a bisa dalilin cewa ya kudirin ya je a makare, daidai lokacin da zaben 2019 ya gabato.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES a lura da cewa Gwamna Rochas Okorocha, wanda INEC ta ce ta soke bayyana shi da aka yi a matsayin wanda yay i nasara, bai halarci bikin bayar da shaidar cin zaben ba.
Hakan na nuni da cewa a yanzu ba sanata ba ne kenan.