Ma’aikatar Ilmi ta gargadi ma’aikatun gwamnati da su rika neman sani game da jami’oin da suke da lasisi Kuma aka amince da shaidar kammala karatun su kafin su rika kushe makarantun.
Hakan ya biyo bayan sukar shaidar kammala karatu na jami’ar Maryam Abacha ne dake Nijar wanda jihar Zamfara tayi.
A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar cewa kada a dauki wani ma’aikaci ko Kuma a kara masa girma a wurin aiki a jihar muddun yana dauke da shaidar kammala karatu daga Jami’ar Maryam Abacha ne.
Hakan bai yi wa jami’ar dadi ba in da bayan samun wannan labari ta fito ta karyata gwamnati jihar Zamfara ta Kuma bayyana wa duniya shaidar amincewa da karatun jami’ar ta samu daga duka hukumomin ba da shaidar ingancin karatun jami’oi ba ma na Najeriya kawai ba har dana kasashen waje.
Ma’aikatar Ilmi ta tarayya ta umarci gwamnatin Zamfara da ta rubuta wa jami’ar shimfidaddiyar wasika na neman afuwa bisa suka da ta yi wa shaidar kammala karatun jami’ar.
” Jami’ar Maryam Abacha na da dukkan satifiket din da jami’a ke bukata domin samun ingancin takardunta kammala karatunta. Kuma ko Ina za a iya amfani da shaidar kammala karatu na jami’ar MAAUN, dake Nijar.
Bayan haka Kuma akwai dangantaka a tsakanin kasar Nijar da Najeriya, da ya had a har da na karatu. You irin wannan katobara zai iya kawo mana matsala a zamantakewar mu ganin cewa an kafa jami’ar a kasar Nijar dinne.
Bayannan hukumar jami’ar MAAUN ta yi Kira ga dalibanta da su yi watsi da wannan Kira na gwamnati Zamfara cewa shaidar kammala karatu na jami’ar ya inganta a ko Ina a fadin duniya.
Jami’ar Maryam Abacha ta samu karbuwa matuka musamman ga dalibai daga kasashen Afrika.
Sannan ta samu lambar yabo ba a can kasar Nijar ba har da Kasa Najeriya da kasashen duniya.
Jami’ar na gab da bude wani sashen karatun koyan aikin asibiti a garin Kaduna wanda nan ba da dadewa ba za a kaddamar da wannan makaranta.