Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa Kungiyar Shugabannin Kiristoci ta Najeriya (CAN), cewa zai bar Najeriya fiye da lokacin da ya same ta a cikin 2015.
Buhari ya yi wannan tabbaci ne a lokacin da kungiyar ta ziyarce shi a fadar sa, bisa jagorancin Shugaban CAN, Samson Ayokunle.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da kawo gyara kan muhimman kalubalen da suka addabi kasar nan, ciki kuwa har da matsalar tsaro, ta tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa.
Kafin sannan sai da shugabannin na CAN suka shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa cewa sun je ne domin su taya Buhari murnar sake lashe zabe karo na biyu da ya yi.
Cikin wani jawabi da kakakin fadar shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya shaida wa maziyartan cewa sakamakon zaben da aka gudanar na shugaban kasa ya nuna yadda dimbin ‘yan Najeriya su ka yi amanna da shugabancin sa.
“Kuma za mu ci gaba da tabbatar da dorewar zaman lafiya, lumana da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.
“A bangaren raba mukamai kuwa, za mu duba cancanta da kuma maida hankali a kan kowane yanki na kasar nan, ta yadda kowane yanki zan san cewa ana tafiya tare da shi.
“Mu na kuma kara kaimi sosai wajen yaki da ta’addancin Boko Haram, tare da kara himma wajen ganin an kubutar da dukkan wadanda ke tsare a hannun Boko Haram din.” Inji Buhari.
Ya kuma jinjina wa CAN a bisa namijin kokarin ta na tsawon shekaru hudu da a lokacin gwamnatin sa ta taka rawa wajen ganin an dinke baraka an kuma kara samun fahimtar juna tsakanin addinai.