Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yanke shawarar rika gudanar da Sallar Juma’a ce a Masallacin Fadar Shugaban Kasa, maimakon Babban Masallacin Abuja, saboda kada ya takura wa jama’a dake harkokin su ganin sai an tattare hanyoyi.
Ya yi wannan jawabin ne bayan da tawagar Limamai da Manyan Malaman Musulunci sun kai masa ziyara tare da neman ba’asin dalilin daina zuwan na sa.
Babban Limamin Babban Masallacin Abuja, Shehu Galadanci ne ya jagoranci tawagar, inda suka kai masa ziyarar jiya Juma’a.
Sau da dama jerin motocin shugaban kasa su na haifar da tsaikon zirga-zirgar motoci a duk lokacin da ya fita daga fada zuwa halartar wani sha’ani a cikin Abuja.
Wannan ya haifar da yawan korafi da suka da jama’a da dama keyi, musamman masu bata lokacin a cikin motoci sun a jiran sai lokacin da Buhari da tawagar sa suka wuce, sannan su kuma za a ba su hannu su wuce.
“Dangane da rokon da ku ka yi min na rika halartar sallar Juma’a a Babban Masallacin Abuja, ina jan hankalin ku da ku lura cewa ni kankin kai nan a fara halartar sallar Juma’a a cikin Masallacin Juma’a na cikin Fadar nan.
Saboda kawai a rage wahalhalu da kunci da takurar da jama’a ke fuskanta.
Haka ya shaida musu a ziyarar da suka kai masa domin taya shi murnar lashe zaben 2019.
Buhari ya ce zirga-zirgar shugaban kasa ta na tattare da ka’idoji da lamurra na sha’anin tsaro. Shi ya sa ya yanke shawarar rika yin sallar Juma’a a Fadar sa.
Buhari ya gode masa dangane da addu’o’in da suka rika sheka masa, sannan ya kara shan alwashin cewa zai kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar nan, musamman ma ta al’amurran da suka shafi tsaro.