AIKIN GAMA YA GAMA: INEC ta bayyana Ganduje ne ya ci zaben Kano

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar APC.

Ganduje ya yi rashin nasara a zaben da aka gudanar na ranar 9 Ga Maris, inda Abba Yusuf na PDP ya ba shi ratar kuri’u 26, 655.

Amma a zaben da aka maimaita ranar Asabar da ta gabata, a cikin kananan hukumomi 28, Ganduje ya samu kuri’u 45,876, shi kuma Yusuf ya samu 10,239.

Haka dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana.

Da ya ke fadin sakamakon zaben, Babban Jami’in mai bayyana sakamako, Bello Shehu, ya ce gaba daya Ganduje ya samu kuri’u 1,033,695. Shi kuma Abba ya samu 1,024,713.

Ya yi wannan sanarwa a hedikwatar INEC ta Kano a yau Lahadi da dare.

INEC ta ce ratar kuri’u 8,982 ne a tsakanin su.

An dai yi mummunan hargitsi a yayin zaben tare da ayyukan ta’asa da harigido da hauragiya da hana masu adawa zabe.

An rika sarar ‘yan adawa da adduna da takubba.

A wasu wurare an ga maza su na jefa kuri’a da katin mata.

Wasu kuma bakin jama’a ne da ba ‘yan mazabar ba suka dangwale kuri’u.

Amma Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Anthony Micheal da aka tura Kano daga Abuja domin zabe, ya ce an gudanar da zaben lami lafiya.

Jam’iyyar PDP ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba. Ta ce zata garzaya kotu domin abi mata hakkin ta.

Share.

game da Author