Ina godewa Kanawa da suka sake bani damar shugabantar su – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya godewa mutanen jihar Kano bisa dama da suka sake bashi ya jagoranci jihar a karo ta biyu.

Ganduje ya bayyana cewa mutanen jihar sunyi na’am ne da irin romon deimokradiyya da yake ta kwarara musu lungu-lungu, kwararo-kwararo shine ya sa suka ga yafi dacewa da ya shugabance su a jihar suka fito suka zabe shi.

Ya bayyana cewa lallai ba zai yi kasa-kasa ba wajen ganin ya sassaka wa dadanda suka zabe shi har da ma wadanda basu zabe shi ba sannan zai yi gwamnati ne na kowa da kowa.

Idan ba a manta ba a jiya ne a aka bayyana zaben gwamnan jihar Kano inda gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ya yi nasara a zaben.

Ganduje ya samu kuri’u miliyan 1,033,695 inda ya ba abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Abba Yusuf ratar kuri’u 8000 da yan wani abu.

Wannan zabe dai an koka a kan sa cewa jami’an tsaro ba su yi adalci ba a zaben.

Share.

game da Author