Kada ayi gaggawan bayyana sakamakon Kano da aka yi wa PDP karfa-karfa – Abba Gida-Gida

0

Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta yi Kira ga hukumar zabe da kada ta yi gaggawar bayyana sakamakon zaben Kano da aka kammala a karshen wannan mako.

A jimlar sakamakon zaben da aka tattara gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 1,033,695, shi Kuma Abba Yusuf na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 1,024,713. Hakan ya nuna cewa APC ta ba PDP ratar kuri’u 8,982.

Abba Yusuf ya bayyana cewa bayyana wannan sakamako da aka danne wa PDP da karfin tsiya zai iya tada rikici a jihar Kano.

Abba ya ce abinda ya dace hukumar zabe ta yi shine ta bayyana PDP a matsayin jam’iyyar da ta yi nasara a zaben.

Idan ba a manta ba, Abba Yusuf na jam’iyyar PDP ya ba Ganduje na jam’iyyar APC ratar sama da kuri’u 26,000 kafin a maimaita zaben da aka you a karshen wannan mako.

Kungiyar Kare Dimokradiyya ta CDD, ta bayyana rashin jin dadin yadda aka tabka hauragiya, shirme da ta’addanci da sunan zabe, a jihohin da aka sake gudanar da zabukan da ba su kammalu ba.

An gudanar da zabukan ne a wasu sassan jihohin Sokoto, Kano, Filato, Bauchi da Benuwai. An jima yi na wasu daidaikun majalisar dokoki a jihohin Lagos da Imo da kuma FCT, Babban Birnin Tarayya.

CDD ta ce ta baza jami’an ta ‘yan sa ido a dukkan wuraren da aka sake zaben, kuma sun aika wa Cibiyar Tattara Bayanai na CDD da tulin bayanai marasa dadin ji da gani.

Ta ce an yi aringizon kuri’u, an yi hargitsi, an ci zarafin masu adawa, musamman a Kano, kuma an yi cinikin kuri’u sosai fiye da misali.

CDD ta ce an rika lakada wa ‘yan adawa dukan tsiya tare da saran su da adduna da takubba, da kuma yankar su da wukake.

Ba a nan CDD ta tsaya ba, ta ce an tarwatsa jama’a a rumfunan zabe tare da ingiza ‘yan-sara-suka domin su tayar da hankulan jama’a ta yadda za a yi magudin zabe.

Kungiyar sa-idon ta kara da cewa an ci zarafin jami’an zabe da kuma ‘yan jarida, musamman a Mazabar Gama, cikin Karamar Hukumar Nassarawa, Jihar Kano.

An kuma rika ganin dandazon ejan-ejan na jam’iyyar APC masu tarin yawa a kowace rumfar zabe.

CDD ta ce an yi amfani da masu dauke da muggan makamai a Nassarawa, Dala, Karaye, Gaya da wasu ka na nan hukumomin Kano da yawa, inda aka maimaita zaben.

CDD ta ce daga cikin ayyukan sa-idon da ta tura ma’aikatan ta su yi a lokacin zaben, sun hada lura da lokacin da aka fara zabe. lokacin da jami’an zabe suka isa, yadda ake tantance masu zabe, yadda ake zabe, yadda ake tattara zabe, yanayin tsaro sai kuma yanayin magoya bayan jam’iyyu.

Share.

game da Author