Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi kira ga matasa da su guji yin ganganci da wauta wai don murnar Buhari ya ci zabe.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Yakubu Sabo ya fadi haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a garin Kaduna.
Sabo yace yin wannan kira ya zama dole ganin yadda mutane ta ta yin tukin saida rai a tutunan Kaduna don murnar nasarar da Buhari ya samu a zaben Asabar din da ta gabata.
” Za mu kama duk wanda muka gani yana tukin gaganci da sunan murnar nasarar cin zabe a titunan Kaduna.”
Sabo ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ahmad Abdurrahman ya yi kira ga iyaye da masu unguwanni da su rika ja wa matasa kunne game da yin hakan.
Ya ce rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da hada hannu da sauran jami’an tsaro a jihar domin samar da tsaro.
Idan ba a manta ba Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabin godiyar sake samun nasarar zama shugaban kasa karo na biyu, bayann sanarwar yinn nasara da INEC ta yi da asubahin yau Laraba.
A cikin jawabin, Buhari ya gode wa daukacin ‘yan Najeriya, kuma ya gode wa musamman Jigon APC Bola Tinubu, Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole da Daraktan Kamfen, Rotimi Ameachi.
Shugaba Buhari ya kuma gode wa dimbim jama’ar da suka bayar da gudummawa a lokacin kamfen din sa a fadin kasar nan.
Sannan kuma ya gode wa wadanda suka sadaukar da kan su da lokutan su da dukiyoyin su wajen tabbatar da ganin an gudanar zaben cikin nasara.
Ya ce duk da cewa an gudanar da zabe lafiya, an samu tashe-tsahen hankula wasu wurare jifa-jifa, inda wasu batagari suka tayar da fitintinu.
Ya ce za a hukunta duk wanda ke da hannu wajen tayar da zaune tsaye a lokacin zabe.
Buhari ya nuna takaici da bacinn rai ganin yadda wasu suka rasa rayukan su sanadiyyar wannan zabe. Sai ya sha alwashin cewa za a kara tabbatar da jami’an tsaro sun karfafa kare lafiyar jama’a a zabubbuka masu zuwa.
Ya gode wa jami’an tsaro da masu sa-ido na gida da wadanda suka zo daga kasashen waje.
Sannan kuma ya sha alwashin ci gaba da karfafa inganta tattakin arziki, yaki da rashawa da magance matsalar tsaro a fain kasar nan.
A karshe ya ja kunnen magoya bayan sa kada murnar cin zabe ta sa su rika tozarta ‘yan adawa.