2019: Babu yadda za a yi kuri’un Atiku su kai shi ga samun nasara – Niboro

0

Tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar zaben da ya samu.

Niboro, wanda kuma shi ne Darakta Janar na Kamfen din Buhari na Gida-Gida, wato Door-to-door, ya shaida wa manema labarai a Warri cewa babu yadda za a yi kuri’un da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya samu su sa har ya ci zabe a kasar nan.

Ya ce matsawar dai aka ce siyasa za ta ci gaba a kan turbar da ta ke tafiya a bisa tsari a yanzu, to ko sai dai a mafarki ne PDP za ta iya sake yin nasara a siyasat Najeriya.

A kan zaben gwamna kuwa, Niboro ya ce APC na da gwamnoni 22, PDP 13, sai APGA guda daya.

Sai ya kara da cewa, “Babu wani gwamnan da ke kan mulki da zai yarda ya fadi zabe. Kai ko da ya kammala wa’adin sa, to zai tabbatar wanda ya ke so ya gaje shi ne ya yi nasara.”

Ya danganta faduwa zaben da Sanata Bukola Saraki ya yi da cewa karfin taron dangin da ‘yar uwar sa Gbemi da Lai Mohammed da kuma iyalan Abdulrasak masu karfin tarin dukiya su ka masa ne.

Ya ce irin guguwar da ta kayar da Saraki, ita ce dai ta kayar da Godswill Akpabio da Emmanuel Uduaghan a yankin Kudu maso Kudu.

Share.

game da Author