ZAZZABIN LASSA: Mutane 120 sun kamu da cutar, 15 sun mutu a jihar Ondo – NMA

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya dake jihar Ondo (NMA) Wale Oke ya bayyana cewa tsakanin watannin Janairu zuwa Fabrairu mutane 120 sun kamu da zazzabin Lasa sannan 15 sun rasu a dalilin haka.

Oke ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Akure.

Ya ce bincike ya nuna cewa kananan hukumomin Owo, Ose, Akoko ta Arewa, Akure ta Kudu da Akure ta Arewa na daga cikin garuruwan dake fama da cutar.

” A watan Janairu mutane 82 ne suka kamu da cutar sannan mutane 15 sun rasu a dalilin kamuwa da ita. A watan Fabrairu kuma mun samu karin mutane 20 da suka kamu da cutar.

” Rashin zuwa asibiti da wuri da shan magani ba tare da izinin likita ba na daga cikin matsalolin da ya sa mutane mutuwa.

Oke yace NMA ta hada hannu da Hukumar NCDC da sauran kungiyoyin kiwon lafiya domin ganin an dakile yaduwar cutar a jihar.

” Muna bi asibitocin dake kananan hukumomi domin wayar da kan mutane game da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar inda a yanzu haka mun kammala da karamar hukumar Akoko.

Hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin lasa sun hada da;

1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.

2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.

3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.

5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.

Share.

game da Author