SANATAN GOMBE TA AREWA: Gwamna Dankwambo ya sha kaye

0

Gwamna Ibrahim Dankwambo na Jihar Gombe, ya sha kaye a kokarin sa na neman kujerar sanatan Gombe ta Arewa.

Ya sha kaye ne a hannun dan takarar APC, Sa’idu Alkali, a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Umar Gurama, daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Kushere, Gombe, ya ce APC ta yi nasara da kuri’u 152,546.

Ya ce shi kuma Gwamna Dankwambo ya tashi da 88,016 a zaben na shiyyar sanatan yankin su na Gombe Ta Arewa.

Shi ma dan takarar APC na Majalisar Tarayya mai suna Yaya Tongo, shi ya yi nasara a zaben Kananan Hukumomin Kwami, Funakaye da Gombe.

Tsohuwar Minista Aishatu Dukku ce ta yi nasarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Nafada da Dukku.

Share.

game da Author