Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Ondo.
A sakamakon zaben da aka bayyana a garin Akure da safiyar litinin din yau, Atiku ya samu kuri’u 275,901 shi kuma Buhari ya samu kuri’u 241,769.
Amma kuma a jihar Osun, Buhari ne ya lallasa Atiku.
Buhari ya samu kuri’u 347,674 shi kuma Atiku na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 337,377. APC ta doke PDP a kuri’u sama a dubu goma a wannan jiha ta Osun.