Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fara shiga gaban abokin takarar sa, Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Benuwai.
PDP ta lashe kananan hukumomi 10 a cikin 14 da aka bayyana sakamakon zaben su.
Jam’iyyar APC ta samu yin nasara a kananan hukumomi hudu.
PDP ta samu kuri’u 182,968, ita kuma APC ta samu 134,208.
Wasu daga kananan hukumomin da PDP ta yi gabala sun hada da: Ado, Apa, Agatu, Obi, Okpokwu, Buruku, Gwer East, Gwer West, Guma da Logo.
Hudu da APC ta yi galaba sun hada da: Tarka, Ushongo, Ohimini da kuma Koshisha.
Jihar Benuwai na da kananan hukumomi 23.