Henrietta Fore da Phumzile Mlambo-Ngcuka shugabanin UNICEF da UNFPA sun yi kira ga gwamnatocin kasashen duniyan da har yanzu ke yi wa mata kaciya da su kara tabbatar da dokar hana yin kaciya wa mata a kasashen su.
Shugabanin sun yi wannan kira ne ranar Laraba wanda ya fado daidai da ranar hana yi wa mata kaciya ta duniya da ake yi ranar 6 ga watan Faburairun kowace shekara.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu akwai kasashen dake fama da burdudin yi wa mata kaciya musamman a kasashen nahiyar Afrika wanda idan ba an karfafa wadannan doka ba ka iya kawo illa ga ci gaban kasa.
” Yi wa mace kaciya ya hada da yanke wani yanki na gaban mace inda a dalilin haka mace kan shiga matsanacin hali da ya hada da rashin jin dadin jima’I, yoyon fitsari, tabuwan hankali da sauran su.
” Bincike ya nuna cewa akalla mata miliyan 200 a duniya ke fama da wannan matsalar a rayuwa sannan da dama a yanzu haka sun fada cikin wannan matsala a duniya.
A dalilin haka shugabanin UNICEF da UNFPA ke kira ga malaman addini kan hada hannu da su domin kawar da wannan matsalar.
Sun kuma ce za su ci gaba da yin yaki da wayar da kan mata game da illar dake tattare da haka,tsara hanyoyin kare mutumcin su da inganta mata domin su fara cin gashin kansu.
A karshe sun yi kira ga gwamnatocin duniya musamman Najeriya da su ware isassun kudade a cikin kasafin kudin su domin ganin hakan ya faru.