Kungiyar Malaman Jami’o’i na Kasa ASUU ta sanar da janye yajin aiki da fara na tsawon watanni uku .
Kungiyar ta sanar da haka ne bayan zama da tayi da wakilan gwamnati a Abuja.
Shugaban kungiyar Abiodun Ogunyemi, ya sanar da haka bayan kammala zaman.
Ministan Kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa sun cimma matsaya daya ne bayan amincewa da kungiyar tayi na alkawarin saki wa jami’o’in kasar nan naira biliyan 25 domin ayyukan su da gwamnatin tarayya ta yi.
Discussion about this post