PDP ta yi babban Kamu a Kannywood

0

Bangaren magoya bayan Jam’iyyar PDP dake Kannywood ta yi babban Kamu inda shahararren dan wasa kuma daya daga cikin wanda suka yi fice wajen yi wa APC da shugaba Muhammadu Buhari Kamfen a farfajiyar Fina-finan Hausa, Adam Zango ya Sauya soyayyarsa zuwa ga dan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Idan Ba a manta Adam Zango ya taba fitowa karara inda ya fadi a shadfinsa ta Instagram cewa ba a taba bashi ko sisi ba domin yayi wa Buhari Kamfen cewa kauna ce da soyayya suka sa shi ya zama dan gani kashenin Buhari.

Sai dai kuma kwatsam sai ga shi Zango ya rabu da bangaren Buhari ya koma bangaren masu mara wa Atiku baya a farfajiyar fina-finan.

Zango ya saka hoton sa da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar yana rike da hannun sa a shafin sa ta Instagram.

Bayan haka ya yi kira ga masoyan sa da su dawo daga rakiyar APC su tattaru su yi wa Atiku Kamfen.

Tuni har jiga-jigan masoyan Atiku a farfajiyar suka rungumi Zango sannan suka rika yi masa lale-lale marhabin da dawo wa bangare su.

Share.

game da Author