Kotu ta yanke wa mahaifiyar dake cin zarafin ‘yarta hukuncin yi wa al’umma aiki na makonni biyu

0

Kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas ta gurfanar da matar da ake zarginta da lakadawa ‘yarta ‘yar shekara takwas duka kullum rana.

Lauyan da ya shigar da karan Benson Emuerhi yace matar mai suna Vivian Onyekachukwu mai shekaru 38 tana yawan jibgan ‘yar ta ne mai suna Chimaza Onyekashukwu da har takan ji mata ciwo a jiki.

Emuerhi ya ce a ranar 30 ga watan Janairu makwabtan su suka kawo kara a ofishin ‘yan sanda dake Alakuko a dalilin dukan da Vivian ta yi wa Chimaza

” Makwabtan sun ce sun fara jin kukan Chimaza daga karfe 9:30 na dare inda da kukan ya ki tsayawa shine suka dunguma zuwa ofishin ‘yan sanda.

Vivian ta yarda da laifin da ta aikata sannan ta roka da a yi hakuri ba za ta sake ba.

” A cikin haushi nake yi wa Chimaza duka sannan na kan yi haka ne ba don na cutar da ita ba amma don ta gyara kurakuren da take aikata wa .

Alkalin kotun Olufunke Sule-Amzat ya yanke wa Vivian hukuncin yi wa al’uma aiki na tsawon makonni biyu.

Share.

game da Author