Yadda halin ko-in-kula na likitocin Asibitin Abuja ya yi sanadiyyar rasuwar ‘da na – Uwa

0

Wata mata mai suna Judy Akpala ta yi kira ga mutane da su mara mata baya wajen ganin gwamnati ta kwato mata hakinta da babbar asibitin kasa dake Abuja ta tauye mata.

Judy ta bayyana cewa ta rasa babban danta Paul Akpala a dalilin rashin maida hankali ga aiki da ma’aikatan asibitin suka yi.

Ta ce a ranar 23 ga watan Janairu ne wani mai mota ya buge danta Paul yayin da yake tallaka titin Beger a Abuja da karfe hudu na yamma.

” Paul ya fita gida a wannan rana domin rubuta jarabawar shiga jami’ar kasar Canada na daliban da suke neman tallafi ke yi a Otel din Sheraton da karfe uku na rana.

Judy ta ce hankalinta yayi matukar tashi a dalilin rashin dawowar sa gida da hakan ya sa ta fita neman sa.

” Na shiga asibitocin dake kusa da mu sannan na shigar da kara a ofishin ‘yan sanda ko da an sace shi. Kai har gidan radiyo sai da na je.

” Washe gari ina cikin juyayin bacewar dana sai aka kirani cewa yana kwance a asibitin kasa dakje Abuja. Nan da nan na nufi asibitin inda na iske kafafuwar Paul nade a bandeji sannan rai a hannu Allah.

Judy ta ce a nan ne mai motar da ya buge shi ya bayyana cewa ya biya asibitin Naira 20,000 domin kara masa jini sannan ya sanar ‘yan sanda.

Ta ce asibitin ta bukaci su biya Naira 200,000 domin kula da yaron amma sai dai allurai suka rika yi masa tun bayan kwanciyar sa.

” Asibitin sun rubuta gwajin da ya kamata Paul ya yi amma babu wanda aka yi daga ciki saboda rashin kayan aiki.

” Da tura ta kai bango asibitin ta yarda na kaishi wani asibitin domin yi masa gwajin da ya kamata.

” Sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa kitse da jini sun toshe huhun sa cewa idan ba an yi masa fida bane zai iya mutuwa.

Judy ta ce asibitin da suka kai danta gwaji sun yi kokarin yin wannan fida amma ma’aikatan kiwon lafiyar dake tare da su daga asibitin kasa Abuja suka hana cewa yin haka zai sa a kore su daga aiki.

Ta ce ko da suka dawo da shi asibitin Abuja dakin kwanciya aka sake mayar da danta inda bayan ‘yan mintuna goma Paul ya rasu.

Judy ta ce Paul ya yi tsawon kwanaki uku a asibitin yana jinya cewa da a jerin wadannan kwanakin ya sami kulan da ya kamata da bai mutum ba.

Sai dai kuma Asibitin kasa sun musanta haka.

Share.

game da Author