‘Yan sanda sun hako jaririyar da aka bizine da ranta a Jigawa

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri ya bayyana cewa sun hako wata jaririya da aka bizine ta da ranta a jihar.

Jinjiri yace sun hako jaririyar ne bayyan iyayen ta sun shigar da karan cewa ta bace.

Ya ce binciken da suka gundanar ya nuna cewa wani matashi Ashiru Abubakar mai shekara 27 ne ya sace jaririyar da gefan mahaifiyarta mai suna Hussaina Yusuf mai shekaru 20 ya gudu da ita cikin daji ya rufe ta ranta.

Jinjiri yace ashe Ashiru wanda mazaunin kauyen Janbiri dake karamar hukumar Birnin Kudu ne yayi wa uwarta ciki tun a farko.

Ya ce Hussaina ta haihu ranar 1 ga watan Faburairu. Washe gari bayan ta haihu Ashiru ya lallaba ya sace jaririyar ya je birne ta da ranta a cikin wani daji.

” Da yake Allah ya sa jaririyar na da sauran kwana domin kafin mu hako ta sai da ta yi awa 28 a kasa amma an hako da ranta.

Jinjiri yace da uwa da ‘ya na samun kula a asibitin Birnin Kudu sannan shi Ashiru na tsare a ofishinsu domin ci gaba da bincike.

Share.

game da Author