Sanata Godswill Akpabio ya yi gwamnan jihar Akwa Ibom na tsawon shekaru takwas. Bayan ya kammala wa’adin sa cikin 2015, ya shiga takarar sanata, kuma ya yi nasara, duk a karkashin jam’iyyar PDP.
Yana a sahun farkon jiga-jigan PDP da gwamnatin Buhari ta fara kai wa farmaki bayan rantsar da Buhari din cikin Mayu, 2015.
Cikin watan Disamba jami’an SSS sun kutsa gidan sa na Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, suka sanar da cewa sun samu tulin milyoyin daloli da kuma makamai a cikin wani dakin sa.
EFCC ta rika binciken sa dangane da zargin jidar kudaden gwamnatin jihar a lokacin da ya ke gwamna, har naira biliyan 117.
A Majalisar Dattawa, Akpabio ya kasance shugaban masu rinjaye kasancewar sad an PDP.
Tsallen-Badaken da ya yi daga PDP ya koma koma APC ya ba jama’a da dama mamaki. Shigar sa ke da wuya sai jam’iyyar APC da fadar shugaban kasa suka karbe shi hannu bibbiyu.
Cikin kankanin lokaci ya zama dan gaban-goshin shugaban kasa, wanda ya fi kowa kici-kicin kare muradin Buhari, na APC da kuma suka PDP a matsayin jam’iyyar barayi, kamar yadda ya ke yawan furtawa.
Ya sake tsayawa takarar sanata a karkashin APC a wannan karon. Daga cikin irin cika bakin da ya rika yi kafin zabe, ya rika cewa:
“Idan na kasa kawo kuri’un karamar hukumar da aka haife ni, to ko mutu kada a rufe gawa ta a kauyen mu.
“Zubar da girma ne a ce maigida ya tsaya ya na fada da mai gadin gidan sa. Korar sa kawai za ka yi ya fice. Don haka ni fa na dauki gwamna Udom Emmanuel aiki. A ranar zabe zan tsige shi cikin sa’o’i uku da fara zabe.”
Duk da irin cika-bakin da ya rika yi kenan kafin zabe, amma bayan kammala zabe, sai INEC ta sanar da cewa Akpabio ya sha kaye.
A yanzu dai ya na can ya na borin-kunya cewa bai yarda da kayen da aka yi masa ba, zai daukaka kara.