Zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa da ya gudana ranar 23 Ga Fabrairu, ya zo ya wuce, amma kuma ya bar baya da kurar da ta tirnike wani zangon shekaru hudu da wasu ‘yan siyasa za su yi su na cizon yatsan rashin nasarar da ba su samu ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta zakulo wasu fitattaun ‘yan siyasa da sakamakon zaben ya jefa su rijiyar da sai bayan shekara hudu masu zuwa za su kara yin wani tasiri, idan sun yi nasara a lokacin.
BUKOLA SARAKI: Ko an kashe biri, biri ya yi barna
Bukola Saraki ya dade ya na jan zaren siyasar sa. Baya ga gwamnan jihar Kwara da ya yi har tsawon shekaru takwas, Saraki ya yi Sanata sau biyu.
A zangon san a biyu ne aka yi tirka-tirkar da aka zabe shi ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, ba tare da son jam’iyyar APC da Fadar Shugaban Kasa ba.
Tun daga lokacin da aka zabe shi ne ya fada cikin rikici da rigingimu, musamman tun daga irin salon yadda aka zabe shi.
Hada baki da Saraki ya yi da sanatocin bangaren PDP ta yi sandiyyar nasarar zama shugaban majalisa da ya yi. Shi kuma ya saka musu da mukamin mataimakin shugaban majalisa, wanda aka nada dan PDP, Sanata Ike Ekweremadu.
Saraki ya sha fama da rigingimu, tun daga maka shi kotu da gwamnatin tarayya ta rika yi, ana yi masa bi-ta-da-kullin wasu zarge-zargen da aka taba yi masa can baya, har zuwa kokarin da aka yi da rana tsaka a tsige shi da karfin jami’an tsaro na SSS, amma duk ya tsallake tarkon bai afka ba.
Komawar sa PDP ya bakanta wa jam’iyyar APC rai matuka. Fadar Gwamnatin Tarayya ta rika ware shi, shi ma kuma din ya rika kebe kan sa daga gwamnatin tarayya.
Tun daga ranar da aka zabi Saraki a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa har tsawon ranar da zai kammala wa’adin sa, APC da gwamnatin muhammdu buhari ba su taba jin dadin shugabancin sa ba, saboda ya zama kadangaren bakin tulu.
Taron dangin da aka yi wa Saraki, aka kayar da shi a zaben neman sake zama sanata a ranar 23 Ga Fabrairu, ya kawo karshen babakeren da ya yi wa siyasar jihar Kwara, kuma ya kawo karshen tsone idon da ya yi wa gwamnatin Buhari.
Saura da me, Hausawa dai na cewa ko an kashe biri, to biri ya yi babbar barna. Watakila idan ya sake shiri, zai dawo a dama da shi a aben 2023.