Kasar Britaniya ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasar zaben 2019 da ya samu.
Cikin wata sanarwar da Ministan Harkokin Afrika ta bayar, Harriett Baldwin ta ce sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta bayar na sakamakon zabe, ya yi daidai a kirdadon jadawalin da kungiyoyin sa-ido suka yi wa zaben.
Ta ce zaben ya nuna yadda ‘yan Najeriya suka jajirce akan bukatar dimokradiyya sosai.
Sai dai kuma ta yi kira ga wadanda ke jin cewa an yi musu rashin adalci ko magudi da su garzaya kotu su nemi hakkin su, a cikin ruwan sanyi da lalama.
“ Mu na kuma kira ga mahukuntan Najeriya da su da su bi ba’asi da bincikar zarge-zargen inda aka yi magudi domin a dauki tsatstsauran matakai a kan wadanda aka kama da aikata laifin.
Sanarwar na kuma dauke da jaje da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su yayin gudanar da zaben.
Baldwin ta ce ba abin so ba ne a ce ko da mutum daya ya rasa ran sa wurin neman ‘yancin da dimokradiyya ta ba shi.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda rikice-rikice suka rika tashi a wasu jihohi, har da asarar rayuka.