KISAN KIYASHIN KAJURU: Gwamnatin Kaduna ta kafa sansanin gudun hijira a yankin da aka yi rikicin

0

Gwmanatin Jihar Kaduna ta fara kokarin samar wa wadanda rikicin kisan kiyashin Kajuru ya ritsa da su matsuguni.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin na kokarin samar musu da sansanin gudun hijirar da za su zauna kafin zuwa wani lokaci.

Jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun ce ana kokarin samun matsugunin a cikin sa’o’i 72 masu zuwa.

Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, KADSEMA, mai suna Ben Kure ne ya shaida haka ga wakilin PREMIUM TIMES a jiya Litinin da rana.

Za a samar da sansanin masu gudun hijirar ne ga sauran wadanda suka tsira da ran su daga cikin Fulanin da aka yi wa kisan-kiyashi a cikin rugage takwas da ke kewayen Maro da Iri cikin Karamar Hukumar Kajuru.

Kwamandan Rundunar Soja ta Daya da ke Kaduna, Manjo Janar Farouk Yahaya ya shaida wa gwamna yadda aka kashe mutane 66, cikin su mata 12 da kananan yara 22 a kauyukan rugagen Fulani.

Kisan dai ana zargin kabilar Adara ne suka yi shi, a matsayin abin da su suka kira ramuwar gayyar kashe musu mutane 11 da suka yi zargin cewa wasu Fulani sun yi.

Yahaya ya shaida wa gwamna cewa an kama mutane har 37 aka tafi da sub akin rafi, aka yi musu yankan rago.

Tuni da gwamna ya halarci wuriN, kuma ya yi alkawarin cewa za a hukunta wadanda suka yi mummunan kisan.

Jam’ian ‘yan sanda sun bada sanarwar kama mutane shida da ake zargi.

A ziyarar da Kure ya yi a yankin a ranar Lahadi tare da jami’an tsaro, Kure ya bada umarnin a gaggauta kai gidan sauro, katifu da kuma kayan abinci.

Ya kuma gana tare da mazauna yankin inda ya hore su da zaman lafiya da juna su.

Share.

game da Author