CPC ta gargadi mutane da su daina amfani da hodar Jand J

0

Hukumar Kare Hakkin mutane na (CPC) ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guje yin amfani da hodar da kamfanin Johnson & Johnson (J&J) ta ke yi cewa hodar na dauke da sinadarorin dake cutar da kiwon lafiyar mutane musamman mata da jarirai.

Shugaban hukumar Babatunde Irukera ya sanar da haka inda ya kara da cewa kotu a kasar Amurka ta gurfana da kamfanin a bisa laifin rashin wayar sanar wa mutane hadarin dake tattare da amfani da wannan hoda.

Hodar J&J wanda uwaye da yara ke amfani da shi na cutar da mutane a dalilin gauraya sinadarin ‘Carcinogen’ da aka yi wajen sarrafa shi.

Bincike ya nuna cewa sinadarin na kawo cutar dajin dake kama mahaifar mata.

Irukera ya ce a dalilin haka ya zama dole a wayar da kan mutane game da ire-iren kayan shafe-shafen da ya kamata su rika amfani da.

” A yanzu haka kotun na sauraron kararraki sama da 9000 wanda mutane suka shigar game da wannan hodar a kasar Amurka.

Irukera yace CPC za ta hada hannu da NAFDAC da SON domin ganin ta kawar da illar dake tattare da wannan hodar a Najeriya.

Ya ce za a iya tuntubar NAFDAC ko kuma hukumar SON da tambayoyi game da kayan shafan da ya kamata ayi amfani da su domin gujewa fadawa cikin matsala.

Share.

game da Author